A wata ganawa da ya yi da manyan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a fadarsa da ke birnin Washington a jiya Talata, Obama ya amince da gaggauta bayar da makamai ga mayaka ‘yan sunni domin kare sauran yankuna da ke zagaye da Bagadaza bayan fadawar birnin Ramadi a hannun mayakan IS.
Yanzu haka Iraqi tana neman mayakan sa-kai da za su bayar da gudunmuwa domin kwato birnin Ramadi daga hannun Mayakan IS.
Daruruwan mutane ne suka fice Ramadi bayan Mayakan IS sun kwace ikon garin a karshen makon da ya gabata.ABNA